rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Tarayyar Turai Girka Tattalin Arziki

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Turai ta kawo karshen yi wa Girka sassaucin basusuka

media
Friministan Girka Alexis Tsipras REUTERS/Alkis Konstantinidis

Ministocin kudin yankin Turai sun kawo karshen matakin da suka dauka da ke hana yi wa Girka sassauci dangane da basusukan da kasashen yankin ke bin kasar.


A cikin watan jiya ne kasar Jamus ta bukaci a dakatar da sassaucin da ake yi wa Girka saboda sabawa wani bangare na yarjejeniyar da ke tsakaninsu.

Ministocin kudin sun amince sun dai na ci gaba da yi wa kasar sassaucin ne a lokacin wani taro da suka gudanar a birnin Brussels na kasar Belgium, bayan da wani kwamiti da kasashen yankin suka kafa ya bayar da shawarar daukar wannan mataki.

To sai dai sanarwar da ministocin suka fitar na cewa matakin na wucin gadi ne, domin za a iya dakatar da shi matukar aka fahinci cewa mahunkutan Girka sun kauce wa abubuwan da ke kunshe a yarjejeniyar da ke tsakaninsu da kasashen yankin na Turai wadda ta shafi ceto tattalin arzikinta.

A ranar 5 ga watan Disamba ne dai aka amince da wannan mataki da ke yi wa Girka sassauci kan yadda za ta biya basusukan da ake bin ta, to sai dai kwanaki 9 bayan haka, Jamus wadda ke a matsayin kasar da ta fi bayar da gudunmuwar a wannan shiri ta bukaci a dakatar da hakan.

A cewar Jamus, Firaministan Girka Alexis Tsipras ya saba wa yarjejeniyar da ke tsakaninsa da Turai saboda amince da wani shirin biyan tsoffin ma’aikata fansho da kuma batun haraji a kan kayayyakin masarufi da suka yi hannun riga da yarjejeniyar.