Isa ga babban shafi
Faransa-Colombia

Hollande ya yi alkawarin taimakawa gwamnati Colombia

Shugaban Kasar Faransa Francois Hollande ya yi alkawarin taimakawa gwamnatin kasar Colombia kwance bama baman da aka dana a Yankin da aka samu yakin basasa tsakanin dakarun gwamnati da ‘Yan Tawayen FARC.

Shugaban kasar Faransa Francois Hollande
Shugaban kasar Faransa Francois Hollande REUTERS/Inalper Castillo
Talla

Yayin da ya ke ci gaba da ziyarar kasar, Hollande tare da shugaba Juan Manuel Santos sun gana da shugabanin Yan Tawayen, inda ya bayyana goyan bayan sa ga yarjejeniyar da bangarorin biyu suka amince da ita.

Faransa ta bada kashi 20 na kudaden da kungiyar kasashen Turai ta taimakawa Colombia dan kulla yarjejeniyar zaman lafiyar.

A watan da ya gabata Majalisar Dokokin Colombia ta amince da wata doka da ke tayin afuwa ga wasu da ake zargi da aikata kananan laifukka yayin yakin basasar da aka kwashe shekaru ana yi.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.