Isa ga babban shafi
MDD

Shan sigari ya haifarwa duniya asarar dala triliyan daya

Bincike ya nuna cewar zukar taba sigari ya sa duniya tayi asarar kudin da ya kai Dala triliyan kusan daya da rabi wajen kula da lafiyar jama’a a shekarar 2012.

Shan sigari ya haifarwa duniya asarar dala Triliyan daya
Shan sigari ya haifarwa duniya asarar dala Triliyan daya Crédit : CC-by-lanier67
Talla

Masana daga Hukumar Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya da kuma Cibiyar yaki da cutar kansa ta Amurka sun ce tabar na lashe kashi biyu na tattalin arzikin duniya, kuma akasarin su suna shafar kashi 40 na kasashe masu tasowa ne.

Binciken ya nuna cewar akalla Dala biliyan 422 ake amfani da su wajen kula da lafiyar masu zukar tabar a asibitoci.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.