Isa ga babban shafi
Ukraine

MDD ta bukaci a tsagaita wuta a Ukraine

Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya bukaci da a tsagaita wuta cikin gaggawa a kasar Ukraine, yayinda ake cigaba da barin wuta tsawon kwanaki uku tsakanin sojin kasar da ‘yan tawaye.

Jami'an lafiya na kasar Ukraine tsaye bisa tankar yakin sojin kasar bayan kwashe sojojin da suka samu raunuka zuwa wani asibiti da ke karkashin ikon gwamnati a garin Avdiivka, dake yankin Donetsk.
Jami'an lafiya na kasar Ukraine tsaye bisa tankar yakin sojin kasar bayan kwashe sojojin da suka samu raunuka zuwa wani asibiti da ke karkashin ikon gwamnati a garin Avdiivka, dake yankin Donetsk. AFP/ Aleksey FILIPPOV
Talla

An dai tabbatar da mutuwar mutane 19 baya ga wasu da dama da suka jikkata sakamakon rikicin

Wannan dai shi ne tashin hankali mafi muni tun bayan sanya hannu kan wata sabuwar yarjejeniya a ranar 23 ga watan Disamba.

Rikicin na ‘yan kwanakin nan ya bar mutane fiye da 20,000 cikin halin kunci sanadiyar yankewar wutar lantarki da samun ruwan sha.

Kasashen duniya sun bukaci bangarorin biyu da ke fada da juna da su tsagaita wuta ganin rayuwar dubban al’umma da ke cikin hadari saboda tsananin sanyi da ake yi yanzu haka a kasar ta Ukraine.

A ranar Lahadin da ta gabata, rikicin ya barke daga yankin da ke karkashin ikon ‘yan a ware.

A watan Afrilu na shekarar 2014, rikicin Ukraine ya barke tsakanin ‘yan a waren da ke goyan bayan Rasha, da bangaren gwamnati al’amarin da ya yi sanadiyar rayukan mutane kusan dubu goma.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.