Isa ga babban shafi
Jamus

Jamus ta soki Rasha kan Ukraine

Jamus ta soki matakin Rasha, na amincewa da sabon Fasfon da ‘yan tawayen da ke rike da yankuna biyu a gabashin kasar Ukraine, ke amfani da shi.

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel
Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel REUTERS/Fabrizio Bensch
Talla

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Markel, ta ce matakin na Rasha tamkar aminta ne da ballewar yankunan na Donetsk da Luhansk, wanda ke a matsayin barazana ga kasar Ukraine.

Yayinda Angela Markel ke maida martani cikin kakkausan harshe ta ce amincewa da fasfon ‘yan tawayen da Rasha ta yi ya sabawa yarjejeniyar da aka cim-ma ta dawo da zaman lafiya a gabashin Ukraine wadda aka tattauna a birnin Minsk na Rasha.

Kimanin shekara guda kenan da ‘yan tawayen a gabashin Ukraine suka fara amfani da fasfon da suka kirkiro mai kaman ceceniya dana Rasha mai dauke da kawuna mikiya 2.

A ranar Asabar din da ta gabata Shugaban Rasha, Vladmir Putin, ya sanya hannu kan dokar da ta amince da Fasfon, wadda ta bai wa al’ummar yankunan na Luhansk da Donetsk damar shiga Rashan ba tare da takardar Izinin shiga ba, matakin da Ukraine ta bayyana a matsayin tsokana.

To sai dai gwamnatin Rasha ta ce amincewar ta wucin gadi ce kafin zuwa lokacin da za a kammala tattaunawar sulhu don dawo da zaman a Lafiya a gabashin kasar ta Ukraine.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.