Faransa
Kotu za ta fara binciken zargin ko Francois Fillon ya ba matarsa albashi
Masu shigar da kara a Faransa sun soma binciken zargin da ake yi wa dan takaran shugabancin kasar Francois Fillon na biyan makudan kudade ga matarsa da sunan ma'aikaciyar sa.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Talla
Kafofin yada labaran Faransa sun gano cewa matarsa Penelope Fillon ba wani aiki ta yi ba da za ta sami makudan kudaden da yake biyan ta.
Ita kanta Penelope Fillon ta ki fadin irin aikin da ta ke yi ba, wanda ake bata makudan kudade da ake zargi.
Masu shigar da kara sun bayyana cewa za su yi bincike ne ko Francois Fillon ya yi almubazzaranci da kudaden Gwamnati.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu