Isa ga babban shafi
EU-Turkiya

Juncker ya gargadi dawo da hukuncin kisa a Turkiya

Shugaban kungiyar Tarayyar Turai, Jean-Claude Juncker, ya gargadi dawo da hukuncin kisa a Turkiya, wadda ya ce zai haifar da babban Katanga a kokarin da kasar ke yi wajen zama Mamba a EU.

Shugaban EU Jean-Claude Juncker
Shugaban EU Jean-Claude Juncker REUTERS/Christian Hartmann
Talla

A zantawarsa da ‘yan Jaridu Juncker ya ce sake dawo da wannann hukunci babu tabbas ya kawo karshan yarjejeniyar da ake son cim-ma don shigar da Turkiya EU

Kallaman Juncker na zuwa ne kwanan guda bayan Shugaba Recep Tayyip Erdogan na Turkiya ya bukaci amincewar Majalisar dokokin kasar na sake dawo da wannan hukunci bayan kada kuri’ar raba gardama a watan gobe.

Dangantaka tsakanin Turkiya da Turai na tsami a 'yan kwananki nan bayan Kasashen Jamus da Netherland sun hana ta gudanar da gangami zabe ga Turkawa mazauna ketare.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.