Isa ga babban shafi
Birtaniya

Scotland zata kada kuri'ar ballewa daga Birtaniya

Majalisar dokokin yankin Scotland, ta amince da kudurin bai wa shugabar yankin, Nicola Sturgeon, damar neman izini daga gwamnatin kasar Birtaniya a hukumance, domin bai wa al'ummar yankin damar kada kuri'ar raba gardama, kan ballewa daga karkashin kasar. 

Shugabar yankin Scotland Nicola Sturgeon.
Shugabar yankin Scotland Nicola Sturgeon. REUTERS/Russell Cheyne
Talla

'Yan majalisu 69 ne suka kada kuri'ar amincewa da kudurin, yayinda 59 suka ki goyon bayan bukatar.

Shugabar yankin na Scotland Nicola Sturgeon na fatan ganin an kada kuri’ar raba gardarmar a shekara ta 2019 kafin ficewar Birtaniya daga kungiyar tarayyar turai, baki daya.

A gobe Laraba ake sa ran Firaministan Birtaniya Theresa May, zata yi amfani da kuduri na 50, a kundin kungiyar EU, don kaddamar da fara tattaunawa ta karshe, da zata shafe shekaru biyu, wajen kawo karshen zaman da kasar ta yi, tsawon shekaru 44, a cikin kungiyar tarayyar turan.

Tun bayan kada Kuri’ar raba gardamar, da ta bada damar ficewar Birtaniya daga tarayyar turai a shekarar da ta gabata, shugabar yankin Scotland Nicola Sturgeon, ta fara fafutukar ganin yankin ya balle daga kasar, domin a cewarta, yankin bashi da ra’ayin ficewa daga EU, illa tilasta masa hakan da Birtaniya ke yi.

A shekarar da ta gabata dai yayin kada kuri’ar raba gardama, mafi rinjayen mutanen yankin Scotland da na Ireland ta Arewa, basu goyi bayan ficewar Birtaniya daga kungiyar tarayyar turai, EU ba, to amma kuri’un al’ummar Wales da na Ingila suka rinjaye su.

Sakamakon wata kuri’ar jin ra’ayi da aka fitar a makon da ya gabata ya nuna cewa, kashi 46 daga cikin al’ummar yankin Scotland na goyon bayan ballewa daga Birtaniya, sai dai har yanzu yawan bai kai abinda yankin ke bukata ba, domin tabbatar da ballewarsa daga Birtaniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.