Isa ga babban shafi
Rasha

Harin tashar jirgin kasa a St Petersburg ya kashe mutane 10

A kasar Rasha mutane 10 ne suka rasa rayukansu wasu kuma da dama suka jikkata sakamakon fashewar wasu ababe a tashar jirgin karkashin kasa dake birnin Saint Petersburg.

Abin fashewa ya hallaka mutane goma a Rasha
Abin fashewa ya hallaka mutane goma a Rasha REUTERS/Anton Vaganov
Talla

A jawabinsa na farko ga manema labarai kan harin Shugaban Rasha Vladmir Putin ya ce an soma bincike don gano musababbin fashewar kafin ya janjantawa iyalan wadanda harin ya rutsa da su

Bayan mutane goman da haka aka tabbatar da mutuwarsu, akwai wasu sama da hamsin da suka sami rauni sakamakon fashewar da ta haifar da rudani a tsakanin al’umma da ya haddasa cunkoson ababen hawa.

Jami’an agajin gaggawa sun mamaye birnin na Saint Petersburg don kai dauki ga wadanda suka sami rauni tare da tattara gawarwakin mamatan a yayin da aka karfafa matakan tsaro a yankin da abin ya faru.

Tuni dai aka soma gudanar da binciken gano musabbabin harin da ake kyautata zaton baya rasa nasaba da na ta’addanci.

Wannan dai ba shine karon farko ba, da ake kai makamancin wannan hari a Rasha, domin ko a shekara ta 2013 wasu tagwayen hare-haren kunar bakin wake sun hallaka mutane 34 a rana guda.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.