Isa ga babban shafi
Faransa

'Yan sandan Faransa na farautar mutum na biyu kan harin Paris

Kungiyar ISIS ta ce ita ta tura maharin da ya harbe wani dan sandan Faransa har lahira, tare da raunata wasu jami'an biyu a birnin Paris a ranar Alhamis din da ta gabata.

Champs-Elysées wurin da wani dan bindiga ya hallaka jami'in dan sandan Faransa tare da raunata wasu guda biyu a à Paris.
Champs-Elysées wurin da wani dan bindiga ya hallaka jami'in dan sandan Faransa tare da raunata wasu guda biyu a à Paris. REUTERS/Reuters Tv
Talla

Rundunar ‘yan sandan Faransa ta ce yanzu haka jami’anta na farautar wani mutum da ake zargi da hannu cikin kai harin bayan hallaka mutumin farko mai shekaru 39.

Shi dai mutumin da ya kai harin kungiyar ISIS ta bayyana shi a matsayin Abu Yessef, dan kasar Belgium, sai dai hukumomin Faransa sun ce ba zasu bada sunansa ba, kasancewar suna cigaba da bincike.

Yessef ya bude wuta ne kan motar ‘yan sandan Faransa a birnin Paris da misalign karfe 9 na dare, abinda ya razana baki ‘yan yawon bude ido wadanda suka tsere daga wurin.

Wata majiya ta ce ‘yan sandan dake yaki da ‘yan ta’adda sun san shi, domin sun dade suna sa ido akan harkokinsa, kuma bayan harin sun kai samame inda yake zama.

Shugaba Francois Hollande wanda yayi jawabi bayan harin, ya sha alwashin karfafa matakan tsaro, muusamman ganin yadda ake fuskantar zabe a karshen wannan mako.

Yau ne dai Hollande ke jagorantar taron majalisar tsaron kasar yayinda ake dakon gudanar da zagayen farkon babban zaben kasar a ranar Lahadi mai zuwa.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.