Isa ga babban shafi
Faransa

Marie Le Pen da Emmanuel Macron sun yi haduwar ba za ta

A wannan laraba ‘yan takarar da za su fafata a zagaye na biyu na zaben shugabancin Faransa a ranar 7 ga watan gobe, Emmanuel Macron da kuma Marine Le Pen, sun yi haduwar ba za ta a fagen yakin neman zabensu a yankin Amiens wanda ake kallo a matsayin yankin da Marine Le Pen ta fi kowane samun magoya baya a zaben da aka gudanar a shekaranjiya lahadi.

Dan takarar Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron a yankin Amiens.
Dan takarar Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron a yankin Amiens. Reuters/路透社
Talla

Al'ummar da suka taru a birnin dai sun yi ta ihu don nuna adawa ga dan takara Emmanuel Macron da ake hasashen kila shi zai lashe zaben shugabancin kasar ta Faransa.

Macron dai ya kai ziyara Amien  duk da cewa  al'ummar yankin na matukar goyon bayan Marie Le Pen da ra'ayinta na kyamar baki,  a yayin jawabinsa dandazon mutanen sun yi ta ihu suna cewa basa ra'ayinsa, kafin daga bisani Marie Le Pen ta bayyana,al'amarin da ya kara harzuka jama'a.

 A ranar 7 ga watan gobe za'a gudanar da zagaye na biyu na zaben shugabancin kasar ta Faransa inda za'a kara a tsakanin 'Yan takarar biyu.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.