rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Tarayyar Turai Birtaniya Rasha

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Kasashen da kusten na'ura mai kwakwalwa ya shafa sun karu

media
Yawan kasashen da kusten na'ura mai kwakwalwa ya shafa sun karu.

Shugaban rundunar ‘yan sandan kungiyar tarayyar turai EU, Rob Wain-wright, ya ce yawan kamfanoni da manyan ma’aikatun gwamnati da harin kutsen bayanan sirri ta na’ura mai kwakwalwa ya shafa, ya karu daga dubu 125 a kasashe 100, zuwa ma'aikatu dubu 200 a tsakanin kasashe 150.


Kasashen da kutsen yafi shafa, sune Rasha da Birtaniya, inda fasahar mai dauke da illa ke kulle dukkanin muhimman bayanan da ke shafin Intanet ko na’ura mai kwakwalwa ta manyan ma’aikatu, kamfanoni da asibitoci, tare da bukatar tilas a biya dala 300 kafin a samu damar dawo da muhimman bayanan.

Jami’an tsaro a nahiyar turai  sun dukufa wajen gano miyagun da suka kitsa wannan ta’asa, sai dai har yanzu ba’a kai ga fara samun nasarar hakan ba.

A gefe guda kuma, masana tsaro sun yi gargadin cewa mai yiwuwa a sake fuskantar makamancin wannan harin a ranar litinin mai zuwa.

Karo na farko ke nan da aka taba fuskantar irin wannan hari a tarihi, tun bayan fara amfani da na'ura mai kwakwalwa ko Intanet a duniya.