A yau ne Shugaban Faransa zai nada Firaministan kasar
Yau ake sa ran sabon shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya nada Firaministan sa da kuma kai ziyara Jamus dan ganawa da shugabar Gwamnatin kasar Angela Merkel.Shugaban ya sha alwashin hada kan al’ummar kasar wanda zaben da akayi ya rarraba.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Macron mai shekaru 39, ya yi alkawarin ne a lokacin bikin rantsar da shi a matsayin sabon shugaban kasar ta Faransa, da ya gudana a jiya Lahadi a birnin Paris, sati guda bayan nasarar da yayi kan Marine Le Pen, a zaben shugabancin kasar zagaye na biyu.
Daga cikin manyan batutuwan da Macron yace gwamnatinsa zata fi bai wa muhimmanci akwai sabunta tsare tsaren tafiyar da fannin tsaron kasar, yin garambawul a fannin kwadago, sai kuma jagorantar sake saita ginshikan da suka kafa kungiyar tarayyar turai EU.
Macron da ya kuma yi alwashin daukaka ‘yancin Faransawa da dimokaradiyyar kasar, ya zama shugaban kasa mafi karancin Shekaru a tarihin kasar tun bayan Napoleon Bonoparte.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu