rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Rasha Amurka

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Rasha ta zargi Amurka kan kutsen bayanan sirri ta shafin Intanet

media
Kawararru a kasashen duniya sun dukufa wajen magance kutse ta kafar na'ura mai kwakwalwa don satar bayanan sirri. REUTERS/Kacper Pempel/Illustration

Shugaban Rasha Vladmir Putin ya ce kasar bata da hannu cikin gagarumin kutsen bayana sirri da manhanja mai illa kan Komfutocin na manyan ma’aikatu, asbitoci da kamfanoni, sama da dubu 200 da aka yi a kasashe 150.


Putin ya dora alhakin kai harin da ya fara aukuwa tun a ranar Juma’ar da ta gabata, kan kasar Amurka, wadda ya ce kwararrunta ne suka kirkiro manhajar mai dauke da illa.

Kutsen mamaye muhimman bayanan da ke shafin Intanet ko na’ura mai kwakwalwa, shi ne mafi girma da aka taba gani a Duniya, wanda yafi shafar kasashen Birtaniya da Rasha.

Tun a ranar Juma’ar da ta gabata ne dai manhajar mai dauke da illa ta kutsa cikin shafuka masu dauke da muhimman bayanai a manyan bankuna, asibitoci, da manyan ma’aikatu sama da dubu 200 da ke kasashe 150.

A baya dai kasar Amurka ta zargi Rasha da hannu cikin hare-hare ko kuma kutsen satar bayanai masu amfani da shafukan Intanet da aka yi a baya, mafi shahara shi ne wanda aka saci bayanan masu amfani da dandalin Yahoo akalla miyan dari biyar.