Birtaniya ta gargadi yunkurin juyin mulki a Najeriya
Gwamnati Birtaniya ta yi gargadi kan duk wani yunkuri na juyin mulki a Najeriya sakamakon rashin lafiyar shugaban kasar Muhamadu Buhari.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Jakadan Birtaniya a Najeriya Paul Arkwright ya ce duk wanda bai gamsu da yadda gwamnatin kasar ke gudanar da mulki ba toh ya hakura har lokacin zabe domin ya sauya ta, amma ba zasu amince da duk wani yunkuri na kifar da gwamnatin ta hanyar juyin mulki ba.
Wadanan gargadi na zuwa ne bayan wanda rundunar sojin kasar ta yi na cewar wasu 'yan siyasa na mu’amala da sojojin kasar, inda shugaban sojin Janar Tukur Buratai ya bukaci sojojin da ke sha’awar siyasa da su tube kakin su.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu