Isa ga babban shafi
Faransa

Macron ya jagoranci taron ministocinsa na farko

Sabon shugaban Faransa, Emmanuel Macron, a yau Alhamis ya jagoranci zaman farko na majalisar ministocinsa, kwana guda bayan sanar da kafa gwamnatin mai kunshe da ministoci 18 da sakatarorin gwamnati hudu.

Emmanuel Macron da Ministocinsa
Emmanuel Macron da Ministocinsa REUTERS/Philippe Wojazer
Talla

Gwamnatin da Firaminista Edouard Philippe, ke jagoranta, na kunshe ne da ministoci daga manyan Jam’iyun Faransa guda biyu Republican da Socialiste, hadi da masu zaman kansu da wasu daga bangaren kungiyoyin fararen hula.

A cewar ministan hadin kan kasa, Richard Ferrand, makusanci ga shugaba Emmanuel Macron Gwamnati za ta yi aiki ne bisa turbar da aka zabi shugaban a kanta ne wajen aiwatar da manufofinsa.

Yanzu haka dai Faransawa sun zaku suga irin rawar da wannan sabuwar gwamnati zata taka, wajen samar masu da sauki ga rayuwarsu tare da saka masu natsuwa sakamakon fargabar da suke fama da ita ta rashin tsaro da barazanar kungiyar IS.

Taron majalisar ministocin na farko na yau ya bai wa shugaba Macron damar zayyana manyan manufofin gwamnatinsa, a yayin da ake sauran ‘yan makwanni a gudanar da zaben wakilan majalisar dokoki.

Shugaban ya kuma jagoranci taro da majalisar kolin tsaron kasar, a yayin da ake sa ran a gobe Juma’a ya ziyarci dakarun kasar da ke fada da yan ta’adda a Mali, domin jinjina masu kan rawar da suke takawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.