Isa ga babban shafi
Faransa

Macron ya nada Majalisar ministocin sa

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya nada Majalisar ministocin sa wanda ya kunshi 'yan bangaren Socialists da masu ra’ayi irin nasa da kuma 'yan Republican, a kokarin sa na kafa gwamnatin da za ta kunshi 'yan kowanne bangare.

Emmanuel Macron Shugaban kasar Faransa
Emmanuel Macron Shugaban kasar Faransa
Talla

Majalisar ministocin mai dauke da mutane 22 ta saba da ta gwamnatin da ya gada wadda ke dauke da ministoci da yawa, kana kuma ya cika alkawari wajen dai-daita wakilan maza da mata.

Sylvie Goulard ta zama ministan tsaro, inda zata maye gurbin Jean Yves Le Drian wanda zai koma ministan harkokin waje, sai kuma Bruno Le Maire ministan tattalin arziki.

Wasu daga cikin nade nade sun kunshi Gerard Collomb, Magajin Garin Lyon a matsayin ministan cikin gida, Francois Bayrou ministan shari’a, wata tsohuwar 'yar wasan Olympic Laura Flessel a matsayin ministan wasanni.

An nada Nicola Holut, wani dan jaridar da ya yi ta sukar manufofin shugaba Macron a ministan muhalli.

Yau ake saran Majalisar ta gudanar da taron ta na farko.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.