Isa ga babban shafi
Faransa

Macron ya soma nazarin sabbin dokokin kwadago a Faransa

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya gana da shugabannin kungiyoyin Kwadago a kasar domin tattauna manufofin gwamnatinsa kan sabbin sauye sauyen da ya yi alkawalin aiwatarwa a lokacin yakin neman zabensa.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron na ganawa da shugabannin kungiyoyin Kwadago
Shugaban Faransa Emmanuel Macron na ganawa da shugabannin kungiyoyin Kwadago REUTERS/Philippe Wojazer
Talla

Shugaban ya ba kansa wa’adi daga nan zuwa watan Satumba domin cim ma bukatar sake tsara dokokin kwadago kamar yadda ya yi alkawali idan ya ci zabe.

Shugaba Macron dai na kokarin tabbatar da sake fasalta ayyukan kwadago ta hanyar kaucewa dogowar muhawara a Majalisa.

Shugaban ya gana da shugabannin manyan kungiyoyin kwadago guda uku a Faransa domin tattauna manufofinsa na sauya dokokin ayyukan kwadago.

A ranar Laraba Macron zai sake ganawa da shugabannin babbar kungiyar ma’aikata ta kasa federation Medef.

Tun a yakin neman zabensa Macron ya yi alkawarin sake fasalta dokokin kwadago, domin samar da ayyukan yi da ci gaban tattalin arzikin Faransa.

Sabbin sauyen sauyen dai sun hada da ba ma’aikata damar tattauna bukatun aikinsu tsakaninsu da shugabanni da suke wa aiki tare da tursasa biyan ma’aikacin da aka kora ko ya bar aiki kudaden lada.

Zuwa watan Satumba shugaban ke fatar cim ma bukatar. Amma zuwa watan Yuni Macron ke fatar kammala tattara bukatun cim ma dokokin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.