Isa ga babban shafi
Faransa

An zargi wani Ministan Macron da bada alfarma

Wasu Jaridun Faransa sun wallafa wani labari da ke zargin Richard Ferrand karaminin Minista a sabuwar gwamnatin Macron da cin mutuncin ofishinsa ta hanyar amfani da wani kamfanin abokin huldarsa domin ba gwamnatin hayar ofis.

Richard Ferrand karamin minista a gwamnatin Macron
Richard Ferrand karamin minista a gwamnatin Macron RFI/Edmond Sadaka
Talla

Rahotanni sun ce Ferrand ya samu rahusa daga kudaden hayar da aka biya domin kafa wani ofishin gwamnati, matakin da wasu ke diga ayar tambaya akan halayyar Ministan a gwamnatin ta Macron inda sai da aka tantance halayyar Ministocinsa kafin ba su mukamin na minista.

Wasu manyan jaridu a Faransa sun ruwaito cewa karamin ministan kuma na kusa da shugaba Macron ya yi amfani da wani kamfanin abokin huldarsa ta kashin kansa domin ba gwamnati hayar wurin da za a yi amfani da shi domin Ofis.

Rahotannin sun ce hayar ta yi sauki saboda ta hanyar alfarma aka bayar da hayar.

Wata jarida da ake kira The Weekly ce ta fara bugo labarin inda ta wallafa shafinta na farko a twitter a jiya Talata, matakin da ya sa gwamnati ta fito tana kokarin kare Ministan.

Jaridar Le Monde ta ambato Firaministan Faransa Edouard Philippe na kare karamin minstan yana mai cewa gaskiya da amincin Ferrand ba abin shan kai ba ne.

A cewar Firaministan babu cuwa-cuwa ko rashawa ga huldar cinikin da aka yi na karbar hayar.

Sai dai Ferrand bai musanta rahoton zargin ba amma ya ce sun zabi ofishin ne saboda saukin kudin hayar.

Ferrand ne dai sakataren jam’iyyar Macron Republic En Marche, kuma shugaba Macron ya yi alkawalin tabbatar da gaskiya da tsabta da kaucewa alfarma da hanyar azurta dangi da abokan arziki kamar yadda ta faru da François da Marine Le Pen.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.