Isa ga babban shafi
Faransa

Macron zai tsawaita dokar ta baci a Faransa

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya bayyana shirinsa na tsawaita dokar ta baci bayan wata ganawa da ya yi da hafsoshin tsaron kasar jim kadan da harin birnin Manchester na Birtaniya.

Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron
Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron 路透社
Talla

Macron ya ce, zai bukaci Majalisar Dokokin Faransa don amincewa da tsawaita dokar wadda aka kafa a shekarar 2015 bayan mummunan harin ta’addancin da kungiyar ISIS ta kai wa kasar.

Dokar wadda aka kafa ta tun bayan harin da ya hallaka mutane 130 a ciki da wajen birnin Paris a cikin watan Nuwamban 2015, ta bai wa Jami’an ‘yan sandan Faransa damar tsananta bincike da kuma kamen wadanda ake zargi.

Shugaban kasar Emmanuel Macron ya ce, zai bukaci Majalisar Dokoki ta tsawaita dokar ta bacin duk da wa’adinta zai kare a tsakiyar watan Juli mai zuwa.

Macron dai zai nemi tsawaita dokar ce sakamakon harin ta’addancin da ya kashe mutane 22 a birnin Manchester na Birtaniya, lamarin da ya sa ya yi ganawa ta musamman da hafsoshin tsaron Faransa.

Makwanni uku kenan da shugabn Macron ya dare kan karagar mulki, yayin da masharhanta ke cewa, yana kokarin nuna kwarewara ta fannin tinkarar barazanar tsaro bayan ‘yan adawa na ma sa kallon mai rauni a harkar samar da tsaro.

Idan dokar ta samu amincewar Majalisa, to za a ci gaba da aiki da ita har zuwa 1 ga watan Nuwamba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.