Jam'iyyar Macron za ta lashe zaben 'yan Majalisu
Wata kuri’ar jin ra’ayin jama’a ta nuna cewa, jam’iyyar shugaban Faransa Emmanuel Macron za ta iya lashe akasarin kujeru a zagayen farko na zaben ‘yan Majalisu da za a gudanar a cikin watan gobe a kasar.
Wallafawa ranar:
Sakamakon sabuwar kuri’ar ta yau Talata, ya nuna cewa akwai yiwuwar jam’iyyar LREM da kawarta MoDem su samu kashi 29.5 cikin 100, yayin da ake saran Jam’iyyar Republican da kawarta su samu kashi 22.
Kuri’ar ta nuna cewa, akwai yiwuwar Jam’iyyar National Front ta samu kashi 18 kacal a kuri’un da za a kada a watan Juni.
Za a fara gudanar da zagayen farko ne na zaben a ranar 11 ga watan na Juni, yayin da za a je zagaye na biyu a ranar 18 ga watan.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu