rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Ingila Ta'addanci

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Mahara sun hallaka mutane 7 a birnin London

media
Jami'an 'yan sandan birnin London da ke sintiri a kan gadar birnin, inda wasu mahara uku suka yi amfani da mota wajen bi takan masu tafiya a kasa. DANIEL SORABJI / AFP

Wasu mahara sun halaka mutane 6 tare da raunata wasu 48, bayanda sukai amfani da wata mota, wajen bi takan masu tafiya a kasa, a kan gadar birnin London, kafin daga bisani maharan, su kutsa kai, cikin kasuwar Borough da ke kusa, inda suka aukawa duk wanda suka tarar, sara da wuka.


Mai Magana da yawun rundunar ‘yan sandan birnin, Mark Rowley, ya ce, jami’ansu, sun samu nasarar halaka maharan guda uku, wadanda suka ce, suna rataye da damarar abubuwan fashewa, sai dai bayan da aka bincika, sun gano cewar na bogi ne.

Harin na daren jiya Asabar, ya zo ne, bayan wanda a kasa da makwanni biyu, aka kai wani a birnin Manchester, wurin taron waka, inda wani dan kunar bakin wake ya hallaka mutane 22.

Har yanzu dai babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai harin. Wanda tuni magajin birnin London SadiqKhan da Fira Ministea Theresa May sukai Ala wadai da shi.

Wani lokaci a yau lahadi Fira minista May zata jagoranci wani taron gaugawa na majalisar tsaron kasar.