rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

ISIL Birtaniya Ta'addanci

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

IS ta dauki alhakin harin London

media
Gadar London da aka kai hari REUTERS/Dylan Martinez

Kungiyar Mayakan IS da ke da’awar jihadi ta dauki alhakin harin birnin London wanda ya yi sanadiyar kashe mutane 7 da kuma jikkata sama da 40. Harin na zuwa a yayin da ake shirin gudanar da babban zabe a Birtaniya.


Kungiyar IS ta sanar da daukar alhakin harin ne ta kafar yada labaranta Aamaq, inda ta ce wani reshenta ne ya kai harin.

Tuni dai Firaministan Birtaniya Theresa May ta zargi masu tsattsauran ra’ayi da kai harin, tare da shan alwashin murkushe su.

A ranar Asabar ne wasu mahara guda uku suka kai harin a gadar London cikin wata mota.

Maharani sun fito suna yanka mutane, kafin ‘yan sanda su harbe su.

Ministan harkokin wajen Faransa Jean-Yves Le Drian ya ce akwai Bafaranshe guda cikin wadanda suka mutu a harin na London yayin da wasu 7 kuma suka samu raunuka.

Yanzu haka ‘Yan Sanda na tsare da mutane 11 da ake zargi na da hannu a harin.

Kimanin mutane 34 suka mutu yayin da sama da 200 suka jikkata a hare haren da aka kai a London da Manchester cikin watanni uku.

Shugabannin kasashen duniya sun la’anci harin tare da nuna goyon baya ga Birtaniya.