Isa ga babban shafi
Faransa

Paris: Dan kungiyar ISIS ya kai hari da guduma

Jami’an tsaron Faransa sun raunata, wani mutum da ya yi yunkurin hallaka wani jami’ain dan sanda ta hanyar kai masa hari da gunduma a kusa da mujami’ar Notre-Dame da ke birnin Paris.

Jami'an tsaron Faransa cikin shiri a harabar mujami'ar Notre Dame a birnin Paris.
Jami'an tsaron Faransa cikin shiri a harabar mujami'ar Notre Dame a birnin Paris. REUTERS/Philippe Wojazer
Talla

Shaidu sun bayyana cewa maharin ya far-wa jami’in dan sandan ne yayinda yake ihun kiran “wannan tukwuici ne ga Syria.

Rundunar ‘yan sandan Faransa ta ce jami’in nata da maharin ya afkawa da gudumar, ya tsallake ijiya da baya, sai dai ya samu rauni a wuyansa.

Maharin dai bai mutu ba sakamakon harbinsa da wani jami’in dan sanda yayi a kirji, inda bayan sa’a guda da ya shafe kwance cikin jini, aka garzaya da shi asibiti, a nan ne kuma ya ce yana daga cikin mayakan kungiyar ISIS.

Ministan cikin gidan Faransa Gerard Collomb, ya ce an kuma gano wasu wukake tare da maharin hadi da katin shaidar da ke nuna dalibi ne daga kasar Aljeriya.

Akalla mutane 1000 ne ke cikin Mujami’ar ta Notre dame da ke tsakiyar birnin Paris a lokacin kai wannan hari, wanda ya jefa tsoro a tsakanin baki masu yawon bude ido da ke halartar mujami’ar, da akai ittifakin akalla bakin miliyan 13 ne ke halartar ta a duk shekara.

Harin ya zo ne kwanaki uku, bayanda da wasu mahara suka hallaka mutane 7 da raunata wasu 48 a birnin London ta hanyar bi takan masu tafiya a kasa da mota a kan gadar birnin da kuma sukar wasu da wukake a kasuwear da ke kusa.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.