rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Faransa Ta'addanci

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Faransa ta kafa rundunar yakar ta’addanci

media
Shugaban Faransa Emmanuel Macron REUTERS/Charles Platiau

Gwamnatin Faransa ta sanar da kafa wata runduna ta musamman da za ta kunshi zarata daga hukumomin tsaro da kuma tara bayanan sirrin domin yaki da ayyukan ta’addanci a kasar.


Daukar matakin dai ya biyo bayan karuwar hare-haren ta’addanci a kasar, cikin har da harin da wani mutum ya kai wa ‘yan sanda da guduma a jiya laraba, yayin da makwabciyar kasar Birtaniya ke ci gaba da juyayin harin da ya kashe mutane 7 a London

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ce wannan barazana ce da ke kara tabbatar da cewa dole ne a kara daura damara a yaki da ayyukan ta’addanci.

Faransawa uku suka mutu a harin London da wasu guda 7 cikin wadanda suka jikkata.