rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Ingila

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

An bude rumfunar zabe a Burtaniya

media
Al'ummar Burtaniya son soma kada kuri'un su REUTERS/Marko Djurica

'Yan kasar Burtaniya kusan miliyan 47 za su kada kuri’a yau Alhamis, domin zaben 'Yan Majalisu 650 a zaben gama gari da Firaminista Theresa May ta kira.


Tuni masu kada kuri’ar wuri ta gidan waya da suka kai sama da kashi 16 suka kada kuri’un su.

Ana fafatawa ne tsakanin Jam’iyyar Conservative da ke karkashin Theresa May da kuma Jam’iyyar Labour da ke karkashin Jeremy Corbyne.

Sai dai ana hasashen ba lallai zaben ya yi armashi ba, la'akari da matsalar tsaro da kasar ke fuskanta a 'yan tsukukun nan.