rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Birtaniya Ingila

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

An bukaci Theresa May ta sauka

media
Firaministan Birtaniya Theresa May REUTERS/Stefan Wermuth

Firaministan Birtaniya Theresa May na fuskantar kalubale bayan ta kasa samun rinjaye a zaben ‘Yan majalisu da aka gudanar a ranar Alhamis a yayin da manyan 'yan adawa suka bukaci ta yi murabus.


Sakamakon zaben da May ta kira cikin gaggawa ya gurgunta jam’iyyarta a yayin da wasu 'yan adawa ke ganin ba abin da ya rage illa ta yi murabus.

‘Yan adawa da wasu daga mambobin jam’iyyarta ta Conservatives sun yi kira ga May ta sauka.

Shugaban adawa Jeremy Corbyn, ya ce May ta sha kaye a zaben domin ta rasa kujeru da goyon bayan jama’a, abin da ya rage yanzu ta sauka.

Shugaban jam’iyyar Liberal Tim Farron ya ce sakamakon zaben ya tabbatar da gazawar Theresa May.

Firaminsita May ta ce ba za ta sauya manyan ministocinta ba, wanda hakan ke nuna za ta ci gaba da tafiya da ministan Kudi Philip Hammond da Ministan harakokin waje Boris Johnson da ministan tsaro Michael Fallon da na cikin gida Amber Rudd.