rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Faransa

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Kotun Faransa ta soke wani bangare na dokar ta-baci

media
Tun a 2015 aka kafa dokar ta baci a Faransa saboda barazanar hare hare ta'addanci Reuters

Kotun tsarin mulki a kasar Faransa, ta soke wani bangare na dokar ta-bacin da aka kafa a kasar domin yaki da ayyukan ta’addanci. Wannan mataki dai ya biyo bayan karar da wani ya shigar ne a gaban kotu, inda ya ke kalubalantar yadda dokar ke tauye hakkokin jama’a.


Wasu daga cikin bangarorin dokar da majalisar ta yi watsi da su sun hada da sashen da ke bai wa shugabannin kananan hukumomi da kantomomi damar hana shirya zanga-zangar lumana idan ana zaton cewa adadin mahalartanta zai zarta daruruwa.

Kotun tsarin mulkin ta soke bai wa shugabannin kananan hukumomin kasar damar hana wa da kuma kwace takardun da ke bai wa wasu izinin zama a yankunansu saboda dalilai na tsaro.

Hukuncin kotun dai ya biyo bayan karar da wani mutum ya shigar ne a gabanta, bayan da mahukunta a wata unguwa da ke birnin Paris suka hana shi damar ci gaba da rayuwa a inda ya ke saboda dalilai na tsaro.

A karshen shekara ta 2015 ne tsohuwar gwamnatin Francois Hollande ta kafa wannan doka lura da yadda kasar ke fama da ayyukan ta’addanci, kuma ga alama shugaba Emmanuel Macron zai bukaci majalisar dokoki ta tsawaita wa’adin aiki da ita.