rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Italiya Brazil

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

An kama Vincezo Macri jigo a safarar hodar ibilis a Duniya

media
Hodar ibilis da yan sanda suka kama a Turai AFP PHOTO PATRICE COPPEE

Yan Sandan kasar Brasil sun sanar da capke wani kusa a kungiyar nan ta Mafia ta kasar Italiya da aka jima ana nema .

Hakan na a mtsayin babbar nasara ga kasashen dake yaki da safarar hodar ibilis a Duniya.


Yan Sanda sun samu kama Vincezo Macri a filin tashi dama saukar jiragen saman birnin Sao Polo dake kudu maso gabacin kasar ta Brazil dauke da takardun jabu na kasar Venezuela da wani suna can daban.

Vicenzo ya yi kauri suna wajen safarar hodar ibilis,inda aka bayyana shi a matsayin wani kusa da ya taka gaggarumar rawa kama daga shekara ta 2004 zuwa 2015 wajen fitar dama shigo da hodar ibilis daga kasashen Morroco, Netherland, tsibirin Dominicain zuwa Italiya.