rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Tarayyar Turai Birtaniya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Kungiyar Turai Na Fargaban Yadda Za Ta Kasance Bayan Zaben Majalisar Birtaniya

media
Firaministan Birtaniya Theresa May REUTERS/Toby Melvillle

Shugabannin kungiyar Tarayyar Turai na bayyana fargaba gameda gazawar Firaministan Birtaniya Theresa May na samun rinjayen wakilai a zaben kasar da ya gabata, al’amarin daka iya jinkirta tattaunawar ficewar kasar daga cikin kungiyar su.


Cikin wannan wata ne dai ake sa ran fara wannan tattaunawa da zai kai ga ficewar Birtaniya daga cikin kungiyar a watan uku na shekara ta 2019.

Ranar 19 ga wannan wata da muke ciki ake sa ran a fara tattaunawar ficewar sosai.

Sai dai kuma Firaminstan Theresa May ta bayyana cewa sabuwar Gwamnatin na ta za su fara tattaunawa nan da kwanaki goma.