rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Zaben Faransa Emmanuel Macron Faransa

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Macron na kan hanyar samun rinjaye a Majalisar Faransa

media
Jam'iyyar Macron ta lashe zagaye na farko na zaben 'yan Majalisu REUTERS/Stephane Mahehane Mahe

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya dau hanyar samun rinjaye a zauren majalisar dokokin kasar, bayan da jam’iyyarsa ta La Republique en Marche da kawayenta suka yi wa tsoffin jami’iyyu siyasar kasar fintikau a zagayen farko na zaben da aka gudanar a jiyar lahadi.


Fitattun ‘yan siyasar kasar da dama ne suka sha kaye, ciki har da shugaban jam’iyyar Socialist Jean-Christophe Cambadelis da kuma dan takararta a neman shugabancin kasar Benoit Hamon da ya gabata da suka rasa kujeransu.

Jam’iyyar Emmanuel Macron da kuma kawayenta masu tsaka-tsakan ra’ayi, sun samu akalla kashi 32 cikin dari na kujerun da aka yi takara a kansa, kafin ranar lahadi mai zuwa inda za a gudanar da zagaye na biyu wanda zai fayyace makomar kowace jam’iyya.

Kamar yadda aka yi hasashe, jam’iyyar La Republique en Marche za ta iya lashe kujeru 400 zuwa 450 ko ma fiye da haka daga cikin 577 da ake da su a zauren majalisar ta Faransa, lamarin da zai kasance mummunan koma-baya ga tsoffin jam’iyyun siyasar kasar da aka saba da su sama da shekaru 60 a kasar.

Sai dai wani abu da ya so ya rage wa zaben na jiya armashi shi ne karancin fitowar jama’a, inda alkalumma ke nuni da cewa kusan kashi 50 cikin dari na wadanda suka cancanci jefa kuri’a ne suka kaurace wa zaben.