rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Birtaniya Jamus Tarayyar Turai

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Birtaniya na da damar ci gaba da zama a Turai

media
Theresa May, Firaministar Birtaniya REUTERS/Kevin Coombs

Yayin da ya rage mako daya a fara tattaunawar karshe domin ficewar Birtaniya daga kungiyar Turai, yanzu haka Firaminista Theresa May na ci gaba da kokarin kulla kawance ne da sauran jam’iyyun siyasar kasar wanda zai ba ta damar ci gaba da jagorantar gwamnati. To sai dai ministan kudin Jamus ya ce, idan har Birtaniya na bukatar ci gaba da kasancewa a kungiyar, har yanzu ba a makara ba.
 


Michel Barnier wanda kungiyar Turai ta dorawa alhakin jagorantar wannan tattaunawa, ya ce akwai yiyuwar a samu tsaiko wajen farawa, lura da raunin da Theresa May ta yi biyo bayan zaben ‘yan majalisar dokokin da aka yi cikin makon jiya.

Theresa dai ta kira zaben gaggauwan ne domin karfafa matsayinta a fagen siyasar Birtaniya, lamarin da ya zo ma ta da ba zata saboda ta rasa rinjayen da take da shi a majalisar.

Dole ne dai Theresa ta yi kokarin shawo kan sauran ‘yan siyasar kasar kafin fara wannan tattaunawa, yayin da ministan kudin kasar Jamus Wolfgang Schauble, ke cewa idan har Birtaniya ba ta shirya wannan ficewa ba, to har yanzu kofar kungiyar Turai na bude domin ta sake dawowa a cikin dangi.

Babu dai wata alama da ke nuni da cewa Firaministar za ta dawo daga rakiyar wannan batu na ficewar kasarta, to sai dai idan har ta aikata, to za ta yi hakan a cikin wani hali mai matukar wuya.