rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Faransa Birtaniya Ta'addanci

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Faransa da Birtaniya za su dakile ta'addanci a Intanet

media
Firaministar Birtaniya Theresa May da shugaban Faransa Emmanuel Macron

Kasashen Faransa da Birtaniya sun bayyana shirinsu na yin aiki tare domin murkushe masu amfani da kafofin sadarwa na zamani wajen cusa tsattsauriyar akida ga matasa.


Bayan ganawar da shugabanin kasashen biyu Emmanuel Macron da Theresa May suka yi a birnin Paris, Macron ya ce, kasashen biyu sun yanke hukuncin cewar masu kula da kafofin sada zumunta ba sa daukan matakan da suka dace domin dakile ayyukan ta’addanci.

A nata bangare, Theresa May, ta ce gwamnatinta ta fara tattaunawa da kamfanonin kafofin sadarwar na zamani domin dakile yada farfagandar ‘yan ta’adda da ke tasiri a zukatan matasa.

Wannan na zuwa ne bayan hare-haren ta’addancin da aka kai wa Birtaniya a biranen London da Manchester, abin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama da suka hada da kananan yara.

Ita ma dai Faransa na fama da barazanar ‘yan ta’adda da suka kai ma ta wani kazamin hari a shekarar 2015, in da fiye da mutane 250 suka mutu.