rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Birtaniya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Ana binciken musabbabin gobarar London

media
Dogob Benen da ya kone kurmus a London Reuters

Gwamnatin Birtaniya ta yi alkawarin gudanar da bincike kan mummunar gobarar da ta tashi a wani dogon bene mai hawa 24, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane akalla 17.


Har yanzu dai hayaki na ci gaba da tashi a ginin na Grenfell Tower, yayin da jama’a ke tambayar gwamnati kan yadda gobarar ta auku.

Ana tunanin akwai yiwuwar adadin jama’ar da suka mutu ya karu, lura da cewa har yanzu ba a ji duriyar wasu ba da gobarar ta ritsa da su.

Mutane da dama ne suka jikkata wadanda har zuwa yanzu ba a iya tantance adadinsu ba, kodayake hukumomin lafiya sun ce mutane kusan 50 ke kwance a gadon asibiti.

Rahotanni sun ce, akalla jami'an kwana-kwana 200 ne ke aikin kashe gobarar, tare da ceto mutanen da suka makale a ginin na Grenfell Tower.

Jami’an kashe gobara sun danganta al’amarin a matsayin mafi girma.