rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Faransa

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Faransa : Mahaifin yaron da aka kashe a 1984 ya gurfana a kotu

media
An tsinci gawar Gregory a cikin kogi shekaru sama da 30 da suka gabata bizarrepedia

A kasar Faransa, kotu ta sake bijirowa da wata tsohuwar shari’a dangane da kisan da aka yi wa wani karamin yaro Gregory Villemin a shekarar 1984 a garin Dijon da ke gabashin kasar. Tuni dai mahaifin yaron mai suna Jean-Marie Villemin ya gurfana a gaban alkali domin amsa tambayoyi dangane da wannan batu.


A ranar 16 ga watan Oktoban 1984 ne aka tsinci gawar Gregory Villemn mai shekaru hudu a duniya a cikin wani kogi, hannuwa da kafufuwansa a daure, sai dai bayan share shekaru ana bincike ne aka jingine wannan batu sai a wannan karo.

Masu binciken, sun gayyaci mahaifin wannan yaro Jean-Marie Villemin, da Marcel Jacob wanda kawun Jean-Marie ne, da matarsa mai suna Jacqueline da kuma wata matar mai suna Ginette da ake zaton cewa samun wasu muhimman bayanai daga gare su kan faruwar wannan lamari.

Sake dawo da wannan batu dai ya biyo bayan wani bincike ne da jandarmomi suka gudanar dangane da wasu bayanai da ke nuni da cewa abu ne mai yiyuwa, daya daga cikin ‘yan uwan Gregory ne ya daure shi tare da jefa shi a cikin kogi.

Shekaru biyu kafin wannan kisa, iyalan gidan sun samu wasiku da dama da ke barazana ga rayuwar wannan yaro mai shekaru 4, yayin da aka sake samun wata wasika kwana daya bayan mutuwarsa da ke daukar alhakin kisan a matsayin na daukar fansa.