Isa ga babban shafi
Faransa

An kai wa tsohuwar minista hari lokacin yakin neman zabe

Wata tsohuwar minista a Faransa Nathalie Kosciusko, ta fita hayyacinta har na tsawon mintuna da dama, bayan da wani mutum ya ture ta har ta fadi a lokacin da take yakin neman zabe a jiya alhamis.

Nathalie Kosciusko-Morizet tana yakin neman zabe a Paris, ranar 15 ga watan yunin 2017.
Nathalie Kosciusko-Morizet tana yakin neman zabe a Paris, ranar 15 ga watan yunin 2017. GEOFFROY VAN DER HASSELT / AFP
Talla

Nathalie Kosciusko-Morizet, tana gudanar da yakin neman zabe ne a cikin watan kasuwa lokacin da wani mutum mai kimanin shekaru 50 a duniya ya afka ma ta tare da warce takardun da ke hannunta sannan ya watsa ma ta a fuska.

Maharin wanda ke nuna fushinsa, ya bayyana Nathalie a matsayin wadda ta tsaya takara domin kare muradun attajirai, lamarin da ya firgita ta har ma ta fadi kasa, sannan ta dauki mintuna da dama kafin ta sake dawowa a cikin hayyacinta.

Bayan wannan hari, mutumin ya ruga a guje inda ya shiga wata tashar jirgin karkashin kasa, yana zargin wannan mata wadda tsohuwar minista ce a karkashin gwamnatin Nicola Sarkozy da cewa tana daga cikin wadanda suka yi sakaci har aka zabi Hidalgo a matsayin magajin garin birnin Paris daga jam’iyyar Socialist.

Daga bisani dai an kwantar da tsohuwar ministar a asibiti domin duba lafiyarta, yayin da ‘yan sanda suka kaddamar da bincike a game da lamarin.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.