rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Tarayyar Turai Faransa Birtaniya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Karuwar ayyukan ta'addanci a yankin Turai

media
Ginin Hukumar 'yan sandan Turai Europol a birnin Hague. LEX VAN LIESHOUT / ANP / AFP

Hukumar ‘Yan Sandan Turai ta ce adadin mutanen da ake kamawa kan zargin alaka da ayyukan ta’addanci a nahiyar Turai ya kusan ribanya abin da aka saba gani shekaru biyu da suka gabata.


Rahotan hukumar ya ce mutane 718 aka kama a shekara da ta gabata, sabanin 395 da aka kama a shekarar 2014.

Sai dai hukumar ta ce an samu raguwar hare-haren da ake kai wa daga 17 a shekarar 2014 zuwa 13 bara, kuma shida daga cikinsu ana danganta su da kungiyar ISIS.

Rahotan mai shafi 62 ya ce mata da yara da kuma matasa sun taka gagarumar rawa wajen kai hare-haren.
Hukumar ta ci gaba da cewa mata da ke kai hari ba sa fuskantar tsananin bincike sabanin takwarorinsu maza, inda ta kara da cewa daga cikin ko wadanne mutane 4 da aka kama a Birtaniya kan zargin ayyukan ta’addanci guda mace ce.

Rahotan ya kuma bayyana Faransa a matsayin kasar da aka fi kama mutane a bara, saboda an kama 456, yayin da aka dakile hare-hare 142.