rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Colombia Ta'addanci

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Colombia: Harin bam ya hallaka mutane 3 a Bogota

media
Jami'an 'yan sandan kasar Colombia tare da, masu sayayya a katafaren shagon saida kayayyaki da ke babban birnin kasar Bogota, Colombia inda aka dasa bam. REUTERS/Jaime Saldarriaga

Mata uku sun rasa rayukansu, wasu 11 kuma suka jikkata, sakamakon wani harin bam da aka kai a wani katafaren shagon saida kayayyaki, a Bogota, babban birnin kasar Colombia.


Magajin birnin na Bogota Enrique Penelosa ya ce daya daga cikin mata ukun da suka mutu a harin ta’addancin, ‘yar kasar Faransa ce.

Jami’an tsaro sun ce an dana bam din ne a wani bandakin mata da ke katafaren shagon saida kayayyakin,

Har yanzu babu wata kungiya da ta yi ikirarin kai harin.

Koda yake a shafinta na Twitter kungiyar ‘yan tawayen ELN, kungiya ta biyu mafi karfi, bayan ta ‘yan tawayen FARC, ta yi ala wadai da kai harin, tare da zargin wadanda ke kokarin dora mata alhakin ta'addancin da yunkurin kawo cikas a tattaunawar sulhun da suke kan yi da gwamnatin kasar Colombia.