rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Birtaniya Tarayyar Turai

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

An fara tattaunawar ficewar Birtaniya daga Tarayyar Turai

media
Wakilin Tarayyar Turai Michael Barnier a tattaunawar ficewar Birtaniya REUTERS

An fara tattaunawar karshe tsakanin wakilan Birtaniya da na kungiyar Tarayyar Turai, domin shata yadda Birtaniya za ta kammala ficewa daga kungiyar kamar yadda ‘yan kasar suka butaka ta hanyar kuri’ar raba gardama da suka kada a bara.


Tattaunawar na zuwa, kwanaki kadan bayan da Firaminista Theresa May ta rasa rinjaye da take da shi a majalisar dokokin kasar, lamarin da ake ganin zai iya haifar wa Birtaniya tarnaki a tattaunawar.

Jagoran tattaunawar a bangaren Tarayyar Turai Michel Bernier ya tabbatar da soma tattaunawar bayan ya gana da ministan Birtaniya David Davis a Brussels a yau Litinin.

Akwai muhimman batutuwa guda uku da Birtaniya ke son tattaunawar ta fi mayar da hankali akai kafin tattauna makomar kawancenta da Tarayyar Turai.

Birtaniya na son Tarayyar Turai ta biya ta kudin ficewa da suka kai biliyan 100 na yuro.

Akwai kuma batun makomar ‘yan kasashen Tarayyar Turai sama da miliyan uku a Birtaniya da ‘Yan Birtaniya a sassan Tarayyar Turai da batun makomar rikicin kan iyaka tsakanin Jamhuriyyar Ireland da arewacin Ireland.