rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Birtaniya Tarayyar Turai

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

An fara tattaunawar ficewar Birtaniya daga Tarayyar Turai

media
Sakataren Birtaniya na ficewa kungiya David Davis tare da Michel Barnier jagoran tattaunawan. REUTERS/Eric Vidal

Kasar Birtaniya da Kungiyar Tarayyar Turai sun fara tattauna batun ficewar Britaniya daga Kungiyar da kafar dama kasancewar sun amince da jadawalin ficewar nan da watan uku na shekara ta 2019.


A tattaunawan farko da suka yi a Brussels Littini Jagoran tattaunawan Michel Barnier ya bayyana cewa taron na su na farko ya yi armashi.

Ya fadawa taron manema labarai cewa sun tsaida ranakun ficewar da tsarin ficewar da muhimman bukatun ficewa daga cikin kungiya.

Ya ce taro na gaba sun tsaida ranar 17 ga watan gobe kuma za su rika tattaunawa duk wata har lokacin da za’a fice dungun daga cikin kungiyar.