rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Ingila Birtaniya Ta'addanci

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

An kai wa Musulmi hari a London

media
An kai wa musulmi hari ne a kusa da masallacin Finsbury arewacin London REUTERS

‘Yan sanda a birnin London sun tabbatar da mutuwar mutum daya yayin da wasu mutane 8 suka samu raunuka bayan da wata mota ta afka a cikin taron jama’a da ke fitowa daga masallaci a cikin daren da ya gabata.


Mutanen London sun taimakawa ‘Yan sanda cafke direban motar mai shekaru 48.

Shugabannin musulmi a London sun ce an yi kokarin kai wa masu ibada ne hari a lokacin da suke fitowa daga Masallacin Finsbury arewacin London dab da Asuba wanda suka danganta a matsayin harin nuna kyama ga addininsu.

Firaministan Birtaniya Theresa May ta danganta harin a matsayin na ta’addanci tare da kiran taron ministocinta na gaggawa domin tattauna harin.

Harin na na zuwa bayan wasu munanan hare hare da aka kai a London ta hanyar afkawa mutane da mota.