rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Portugal

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Portugal na zaman makoki kan gobarar daji

media
Gobarar dajin ta ci mutane sama da 60 a Portugal REUTERS/Rafael Marchante

Gwamnatin kasar Portugal ta sanar da ware kwanaki uku domin zaman makoki a fadin kasar sakamakon mahaukaciyar gobarar daji da ta hallaka mutane masu yawan gaske.


Tun a ranar Asabar ne gobarar ta tashi kuma har ya zuwa lahadi an gaza shawo kanta al’amarin da ake ganin al’ummar kasar ba su taba ganin irin wannan bala’i ba domin komi ba ta bari ba.

A tsawon Lahadi ‘yan kwana-kwana 900 da motocin aiki 300 ke ta hakilon kashe gobarar da ta fara daga yankin Pedrogao Grande.

Da ya ke ayyana fara zaman makoki na kwanaki uku tun daga jiya, Firaministan kasar Antonio Costa ya bayyana kaduwa da wannan gobara da aka rasa shawo kanta cikin gaggawa.

Sakataren Harkokin cikin gida na kasar Jorge Gomes ya fadi cewa yawancin mamatan an same su ne kone kurmus cikin morocinsu, amma ba a sani ko sun yi kokarin tserewa ne wutar dajin ta turke su ba.

Kasar Spain ta kai dauki da wasu jiragen sama biyu masu feshin ruwan kashe gobara.

Wasu jami’an Gwamnati na cewa tsananin tsawa da aka yi ta haifar da gobarar.