Isa ga babban shafi
Turai

Ana zargin mai bai wa Fafaroma shawara da lalata yara

Jami’an ‘yan sandan kasar Australia, sun shigar da kara kan daya daga cikin mashawartan fafaroma Francis a fadar Vatican, wato George Pell, bisa zarginsa da lalata kananan yara a shekarun baya.

Babban na hannun daman Fafaroma Francis a fadar Vatican George Pell.
Babban na hannun daman Fafaroma Francis a fadar Vatican George Pell. REUTERS/Tony Gentile/File photo
Talla

Karo na farko kenan, da aka yi yunkurin tabbatar da wannan zargi kai tsaye a tsakanin manyan limaman fadar Vatican.

George Pell wanda shi ne ministan tattalin arziki a Vatican, shi ne mafi kololuwar masu rike da mukamai a fadar da ya fuskanci wannan zargi na lalata da kananan yara.

Ko da yake Pell mai shekaru 76, ya musanta aikata laifin, tuni aka bashi hutun wucin gadi domin komawa kasarsa ta Australia don wanke kansa daga zargin.

‘yan sandan jihar Victoria da ke kasar Australia, inda Pell a kasance jagoran shugabannin mujami’a sun ce ya tafka barnar ce a tsakanin shekarun 1970 zuwa 1979, bayanda iyayaen yaran da Pell ya lalata da dama, suka bada shiadar hakan.

Har yanzu dai rundunar ‘yan sandan Australia basu fayyace mizanin shekaru na yaran da ake zargin Pell ya lalata ba, ko kuma a ainahin lokutan da hakan ta faru, sai dai kotu ta bashi sammacin ya bayyana a gabanta a ranar 18 ga watan Yuli mai kamawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.