Isa ga babban shafi
Birtaniya

Theresa May ta tsallake rijiya da baya

Firaministar Birtaniya Theresa May ta yi nasara da kyar a kuri’ar da ‘yan majalisar dokokin kasar suka jefa domin amincewa ta ci gaba da yunkurinta na kasancewar shugabar gwamnati.

Firaministan Birtaniya  Theresa May
Firaministan Birtaniya Theresa May Handout / AFP
Talla

Sakamakon samun goyon baya daga wata karamar jam’iyyar da ake kira DUP daga yankin Ireland, Theresa ta samu kuri’u 323 yayin da 309 suka kada kin amincewa daga jimillar ‘Yan mambobi 650 da ake da su a majalisar.

Maya diat a fuskanci kalubale a babban zaben da ta kira na gaggawa da aka gudanar a ranar 8 ga Yuni inda ta rasa rinjaye a majalisar.

Tun gabanin kada kuri’ar Jam’iyyar Conservatives ta May ta kulla kawance da DUP tare da alkawalin cikawa Jam’iyyar alkawalin tallafin kudi na arewacin Ireland da suka rage fam Biliyan daya.

Yanzu ‘Yan majalisar DUP guda 10 za su ci gaba da marawa May baya a muhimman batutuwan da suka shafi Birtaniya.

Dakta Aliyu Musa na Jami’ar Coventry a Ingila ya ce har yanzu akwai kalubale a gaban May musamman hada kan mambobin jam’iyyarta da ke adawa kawancen da ta kulla da jam’iyyar DUP saboda banbancin akidunsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.