Isa ga babban shafi
Jamus

Tarayyar Turai ta karrama Helmut Kohl na Jamus

Shugabannin Kungiyar Tarayyar Turai, sun yi bikin karrama tsohon shugaban gwamnatin Jamus Helmut Kohl da ya rasu a watan Yunin da ya gabata, musamman kan irin gudunmawar da Kohl mai shekaru 87 ya bayar, wajen hadin kai, da bunkasar tattalin arzikin Turai

An karrama Kohl a Majalisar Turai
An karrama Kohl a Majalisar Turai ©REUTERS/Arnd Wiegmann
Talla

Karo na farko ke nan da majalisar Tarayyar Turai ta karrama wani tsohon shugaba a lokacin bikin binne shi kamar yadda ta yi wa Helmut Kohl a birnin Strasburg wanda ya shugabanci gwamnatin Jamus daga shekarar 1982 zuwa 1998.

Daga cikin manyan abubuwan tahirin da Kohl ya aiwatar a nahiyar Turai, akwai hada kan yammaci da gabashin Jamus da ya jagoranta, bayan rushewar katafariyar katangar da ta raba yankunan biyu a shekarar 1989.

Helmut Kohl ya bada muhimmiyar gudunmawa, wajen kafa kungiyar Tarayyar Turai da kuma kirkirar tsarin amfani da takardar kudin bai daya ta yuro tsakanin mambobin kungiyar.

Sama da mutane 600 suka shaida bikin karrama gawar Kohl a wajen zauren majalisar Tarayyar Turai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.