rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya
Gaggauce
Kotun Kolin Najeriya ta tabbatar da nasarar Ganduje a matsayin gwamnan Kano

Turkiya Girka

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

An samu girgizar kasa mai karfin maki 6.7 a Turkiya da Grika

media
Girgizar kasa mai karfin maki 6.7 aTurkiya da Grika Yasar Anter/Dogan News Agency via REUTERS

Girgizar kasa mai karfin maki 6.7 ta yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama tare da raunata wasu akalla 360 a kasashen Turkiyya da kuma Grika, kamar dai yadda majiyoyin kiwon lafiya suka tabbatar.


Girgizar kasar ta afka wa tsibirin Kos na Girka yayin da ta wuce har zuwa wani tsibiri mai suna Bodrum mallakin kasar Turkiya inda ta haddasa barna ga gine-gine da kuma katsewar wutar lantarki a garuruwa da dama.

Ministan kiwon lafiya na kasar Turkiya Ahmet Demircan, ya ce a kauyukan da ke kan tsibiirin Bodrum kawai, sama da mutane 300 ne aka kwantar a asibitoci sakamakon raunukan da suka sama.

A tsibirin Rhodes mallakin kasar Girka, jami’an tsaron sun tabbatar da mutuwar mutane biyu, daya dan Sweden da kuma wani dan Turkiya wadanda lamarin ya rutsa da su a lokacin da suke yawon bude ido.

Wannan girgizar kasa ta haddasa fargabar yiyuwar samun igiyar ruwa irin ta Tsunami, lamarin da ya sa mahukunta daukar matakin gagawa domin fara kwashe jama’a daga garuruwan da ke gabar ruwa.