Isa ga babban shafi
Faransa

Faransa ta nemi agaji domin kashe wutar daji

Sama da mutane dubu 10 ne aka kwashe daga yankin da wutar dajin ta shafa, lura ida yadda gobara ke saurin yaduwa a cikin kwanaki biyu da tashinta.

Wani jirgin kashe gobara a yankin Carros, kusa da Nice a Faransa ranar 24 ga watan yulin 2017.
Wani jirgin kashe gobara a yankin Carros, kusa da Nice a Faransa ranar 24 ga watan yulin 2017. A Canadair firefighting aircraft drops water on a wildfire which
Talla

Gobarar ta tashi ne a yankin Bormes-les-Mimosas da ke kudancin kasar, yankin da ke jan hankulan masu yawon bude ido sosai a kowace rana ta Allah.

Tuni aka kwashe baki masu yawon bude ido da yawansu ya haura dubu uku daga yankin, yayin da jami'an tsaro da suka hada da 'yan kwana-kwana dubu 4, tare da wasu jiragen saman kashe gobara 19 ke ci gaba da aiki domin murkushe wutar dajin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.