Isa ga babban shafi
Faransa

Majalisa ta bai wa Macron damar aiwatar da sauyi ga dokar kwadago

Majalisar dattawan Faransa ta amince da kudirin dokar da zai bai wa gwamnatin Emmanuel Macron damar aiwatar da sauye-sauye cikin gaggawa a dokokin kwadagon kasar, wanda hakan zai bayar da damar fara zaftare rashin aikin yi a kasar.

Bourbon, ginin Majalisar Dokokin Faransa.
Bourbon, ginin Majalisar Dokokin Faransa. LUDOVIC MARIN / AFP
Talla

Bayan kwashe makonni ana tafka muhawara, majalisar dattijen ta amince a aiwatar da sauye-sauye a dokokin kwadagon kasar bayan cimma daidaituwa da kungiyoyin kwadago da kuma kamfanoni.

 

‘Yan majalisu 225 ne suka yi na’am da wannan sabon tsarin yayin da 109 da suka nuna adawarsu.

 

Shugaba Emmanuel Macron wanda ke da kwarewa  a lamarin da ya shafi bunkasa bankuna, na son bai wa kamfanonni da ma’aikata damar kulla yarjejeniya da ba za ta iya zama cutarwa a gare su ba.

 

Samar da aikin yi shi ne babban abin da Macron ya sanya a gaba, a kasar da ke da mutane sama da miliyan 3 masu zaman kashe wando, inda ya alkawarta rage kashi 9 cikin dari na marasa ayyukan yi zuwa kashi 7 kafin 2022.

 

Gwamnmatin Faransa ta ce aiwatar da sauye-sauye a dokar ya fuskanci suka da farko har daga bangare kungiyoyin kwadago, amma tabbatar da ita zai zama riba ga masu kamfani da kuma ma’aikatansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.