Isa ga babban shafi
Turai

Gurbataccen kwai na yaduwa a Turai

Birtaniya da Faransa sun ce lallai an shigar da gurbataccen kwan kajin da maganin kwari ya lalata zuwa cikin kasashen su, a daidai lokacin da ake kashe miliyoyin kajin da matsalar ta shafa a kasar Netherlands.

Gurbataccen kwai mai dauke da sanadarin Fipronil ya yadu a Turai
Gurbataccen kwai mai dauke da sanadarin Fipronil ya yadu a Turai REUTERS/Hannibal Hanschke/Illustration Photo
Talla

Kasashen Jamus da Netherlands da Belguim da Sweden da Switzerland duk sun kwashe irin wannan kwan domin lalata su.

Ofishin ma’aikatar noman ta Faransa, ya ce yanzu haka suna kan gudanar da binciken gano ko kwan ya shiga kasuwa.

A ranar Assabar da ta gabata mahukuntan kungiyar tarayyar turai suka sanar da Faransa cewa ta yi hattara an shigar mata da wannan gurbataccen kwan.

Tuni manyan shagunan sayar da kayayyakin abinci na kasashen Netherland da Jamus suka janye irin wannan nau’in kwai mai yawan gaske daga kasuwannin su, matakin da ya haifar da asarar miliyoyin Yuro kamar yadda kungiyar masu kiwon kaji ta Nertheland ta sanar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.