Isa ga babban shafi
Korea ta Arewa

Korea ta arewa ta shirya harba makami Amurka

Kasar Koriya ta arewa ta tsara yadda za ta cilla wasu makamanta masu linzami har guda hudu zuwa wani yanki a Japan da kuma yankin Guam na kasar Amurka, matakain da ke kara sanya fargabar barkewar yaki tsakanin Koriya ta arewar da kuma Amurka, bayan daukar lokaci ana musayar kalamai masu zafi.

Shugaban Korea ta Arewa Kim Jong UN na shirin harbawa Amurka makami mai linzami
Shugaban Korea ta Arewa Kim Jong UN na shirin harbawa Amurka makami mai linzami Reuters
Talla

Ana dai ganin Matakin wani raddi ne kan kalaman da shugaban Amurka Donald Trump ya yi na cewa har yanzu kasar na matsayin ja gaba a fannin makamain Nukiliya fiye da kowacce kasa a duniya bayan wata barazanar da Koriya ta arewa.

Koriya dai ta yi barazanar kai hari yankin Guam na Amurka lamarin daya tayar da hankalin mazauna yankin tare da harzuka shugaba Donald Trump.

Trump dai ya ce Amurka ta mallaki manyan makaman Nukiliya fiye da wadanda ta ke da su a shekarun baya, don kuwa a cewar wasa umarnin farko daya fara yi bayan darewarsa karagar mulkin kasar shi ne karfafa bangaren makamin Nukiliya.

Tuni Tarayyar Turai a yau Alhamis ta kara tsawaita jerin takunkumanta akan Koriya ta Arewar da suka hada da toshe asusunta da kuma hana ta shiga kasashen.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.